Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Shiga Iraki Domin Ziyarar Arba'in A Karbala

Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Shiga Iraki Domin Ziyarar Arba'in A Karbala

Kwamandan rundunar tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Mutanen da suka fice daga cikin kasar Iran zuwa ziyarar arba'in a birnin Karbala na kasar Iraki sun kai mutane 1,950,000.

A zantawarsa da manema labarai a yammacin jiya Litinin: Kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran Brigadier Janar Husaini Ashtari ya bayyana cewa: Al'ummar Iran da yawansu ya kai miliyan daya da dubu dari takwas gami da baki 'yan kasashen waje mazauna kasar ta Iran dubu dari da hamsi ne suka fice daga cikin kasar Iran zuwa kasar Iraki domin raya juyayin ranar arba'in ta Imam Husaini jikan manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna {a.s} a hubbarensa da ke birnin Karbala na kasar Iraki.

Janar Ashtari ya kara da cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata ne tawagar jama'a daga Iran suka fara tattaki da kafa zuwa birnin Karbala na kasar Iraki ta kan iyakokin kasar guda uku na Mehran, Chazabeh da kuma Shalamcheh.

Brigadier Janar Husaini Ashtari ya kara da cewa: A shekarar da ta gabata; mutanen da suka tafi raya juyayin arba'in na Imam Husaini {a.s} daga Iran sun kai mutane miliyan biyu da dubu dari uku da hamsin daga cikin al'ummun duniya kimanin miliyan goma sha hudu da suka halacci makokin arba'in a Karbala.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky