Miliyoyin Al'ummar Musulmi Sun Fara Gudanar Da Juyayin Ashura A Sassa Daban Daban Na Duniya

Miliyoyin Al'ummar Musulmi Sun Fara Gudanar Da Juyayin Ashura A Sassa Daban Daban Na Duniya

Miliyoyin al'ummar musulmi musamman mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} sun fara gudanar da juyayi tare da alhinin tunawa da zagayowar ranar Ashura 10 ga watan Muharram, ranar da aka aiwatar da kisan gilla kan jikan fiyayyen halitta Manzon Allah {s.a.w} wato Imam Husaini dan Ali dan Abi-Talib {a.s}.

Ranar Ashura goma ga watan Muharram, rana ce ta juyayi da alhini ga al'ummar musulmi musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsarkaka da kuma 'yantattu a tunani masu dauke da ruhin dan Adamtaka, saboda a irin wannan rana ce a shekara ta 61 bayan hijira, wata al'umma da take riya Musulunci ta dauki matakin aiwatar da kisan gilla ga jikan manzon Allah, daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna Imam Husaini dan Ali dan Abi-Talib {a.s} a filin Karbala na kasar Iraki.

Hakika hadisai daga bangaren musulmi shi'a da sunnah sun tabbatar da yadda fiyayyen halitta, manzon tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} ya zubar da hawaye tare da yin la'ana kan wadanda zasu kashe masa jika bayan da Mala'ika Jibrilu {a.s} ya bashi labarin irin kisan gillar da al'ummarsa zata aiwatar kan jikan nasa a lokacin da ya kawo masa ziyarar bayan haihuwar Husaini {a.s}.

Rahotonni daga kasar Iraki suna nuni da cewa: Miliyoyin al'ummar musulmi daga sassa daban daban na duniya suna ci gaba da yin tururruwa zuwa hubbaren Imam Husaini jikan manzon Allah da ke birnin Karbala domin gudanar da juyayin wannan rana ta Ashura, inda jami'an tsaron kasar suka tsaurara matakan tsaro da nufin kare lafiyar al'umma musamman baki 'yan kasashen waje.

Kamar yadda a kasar Iran da sauran kasashen musulmi gami da kasashen yammacin Turai mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsarkaka {a.s} suke gudanar da zaman makoki da gudanar da zanga-zanga domin jaddada goyon baya ga yunkurin Imam Husaini na kare martaba da kimar addinin Musulunci tare da taya Manzon Allah da iyalan gidansa alhinin wannan rana. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky