MDD Ta Amince Da Shawarar Iran Kan Kwance Damarar Makaman Nukliya A Duniya

MDD Ta Amince Da Shawarar Iran Kan Kwance Damarar Makaman Nukliya A Duniya

Duk tare da kokarin gwamnatin Amurka na hana shawarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan kwance damarar kasashe wadanda suka mallaki makaman nukliya, MDD ta amince da shawarar a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa shawarar kasar Iran tana bukatar dukkan kasashen duniya da suka mallaki makaman nukliyar su lalatasu, kamar yadda dokar hana mallakar makaman Nuklia ta NPT ta bukata.

Har'ila yau shawarar ta bukaci wadannan kasashe su dakatar da kera irin wadannan makaman su kuma daina sayar wa wasu kasashe ko kuma kai su wasu kasashen. 

Kasashe 112 ne, na kwamitin da ake kira (First Committee) a babban zauren MDD suka zabi amince da shawarar, a yayin da kasashe 44 suka ki amincewa da ita, sai kuma wasu kasashe 15 da suka kauracewa zaben.

Kasashen Amurka, HKI, Britania, Rasha da kuma Faransa suna daga cikin kasashen da suka ki amincewa da shawarar.

Gwamnatin JMI ta bada wannan shawarar ce bisa shawarorin da aka gabatar a tarurrukan hana amfani da kuma kera makaman nukliya a shekaru 1995, 2000 da kuma 2010.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky