Masar Tayi Afuwa Ga 'Yan Bursuna 645

Masar Tayi Afuwa Ga 'Yan Bursuna 645

Shugaban kasar Masar yayi afuwa tare da bayar da umarnin sakin 'yan kaso sama da dari shida a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki daga birnin Alkahiran Masar ya habarta cewa shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya bayar da umarnin yin afuwa ga 'yan kaso 645, tare da umartar ma'aikatar cikin gidan kasar ta zartar da wannan umarni.

Umarnin shugaban kasar ya tabbatar da cewa duk wanda ya rage lokacin zaman gidan yarinsa daga lokacin da aka daure shi zuwa ranar zagayowar ranar 'yan sanda da ranar juyin juya halin kasar an yi masa afuwa.

Ma'aikatar cikin kasar ta ce za ta kafa kwamitin na musaman domin gano wadanda wannan afuwa ta shafa, sannan kuma a sake su.

Kasar Masar dai na fuskantar matsalar ta'addanci tun bayan da shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya dare kan karagar milki a shekarar 2013 bayan kifar da gwamnatin Muhamad Mursi


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky