Masar : An Kashe 'Yan Sanda 53 A Saharar Kudancin Kasar

Masar : An Kashe 'Yan Sanda 53 A Saharar Kudancin Kasar

Hukumomi a Masar sun ce 'yan sandan kasar 53 ne suka gamu da ajalinsu a wani artabu tsakaninsu da 'yan ta'adda a yankin saharar kudancin kasar.

Lamarin dai ya auku ne a ranar Juma'a da ta gabata a yayin da 'yan ta'addan suka bude wuta kan jami'an tsaron lokacin da suke atisaye a yankin.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce an kai wa jami'an tsaron harin ne da makamin roka da kuma wasu muggan makamai.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an kashe 15 daga cikin 'yan ta'addan.

Kungiyar nan mai kaifin kishin islama ta Hasm ce ta dauki alhakin kai harin a cewar hukumomin kasar, saidai wasu rahotanni sun ce babu tabbas game da hakan kasancewar babu wani bayyani a shafin Twitter inda kungiyar ta saba fitar da sanarwowinta tun ranar 2 ga watan nan na Oktoba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky