Manufar Makircin Yahudawan Sahayoniyya Kan Masallacin Qudus Da Taimakon Masarautar Saudiyya

Manufar Makircin Yahudawan Sahayoniyya Kan Masallacin Qudus Da Taimakon Masarautar Saudiyya

A daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ke ci gaba da aiwatar da makirce-makircenta kan Masallacin Qudus musamman a cikin 'yan kwanakin nan, wani shahararren malamin masarautar Saudiyya ya furta furucin karfafa yahudawan kan mummunar aniyarsu dangane da Masallacin na Qudus.

Sheikh Ahmad bin Sa'id Al-Qarni daya daga cikin masu bada fatawar hukunce-hukuncen addini a kasar Saudiyya ya yi kira ga al'ummar musulmi musamman Palasdinawa da su kawo karshen duk wata gwagwarmayar yantar da Masallacin Qudus, domin mallakin Yahudawa ne, kuma su kwana da sanin cewa; babu wata kasar Larabawa da zata tura sojojinta zuwa Palasdinu domin 'yantar da Masallacin na Qudus.

Har ila yau wannan furucin sheikhin malamin na kokarin kashe karfin  gwiwar al'ummar Palasdinu da ma al'ummar musulmin duniya kan kare kimar Masallacin Qudus ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta hana al'ummar musulmi gudanar da sallar Juma'a a cikin Masallacin na Qudus a makon da ya gabata, lamarin da ya fusata masallata har ta kai ga bullar wata kwarya-kwaryar tarzoma tare da tofin Allah tsine daga al'ummar musulmi daga sassa daban daban na duniya. 

Matakin rufe Masallacin Qudus a makon da ya gabata ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya take gudanar da rushe-rushe a cikin Masallacin da nufin gina wani bangaren wajen bautar yahudawa. Sakamakon haka Khalil Attafkaji masharhanci kan Palasdinu ke bayyana cewa: Tuni dama gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana kokarin ganin ta maida da birnin Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da rufe Masallacin Qudus ta hanyar hana al'ummar musulmi gudanar da sallah a ciki. Kamar yadda tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida suke da niyyar gina wata majami'arsu ta yahudawan a bangaren mashigar Babur Rahman na Masallacin na Qudus.

A fili yake cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da masu mara mata baya na kasashen yammacin Turai musamman kasar Amurka sun sha kokarin yin amfani da mahukuntan kasashen Larabawa domin sakarwa yahudawan sahayoniyya mara da nufin cin karensu babu babbaka a kan al'ummar Palasdinu da Masallacin Qudus, amma a halin yanzu da maitar mahukuntan Saudiyya ta fito fili musamman a kokarin da Sarki Salmanu ke yi na gudanar da garanbawul a tsarin masarautar kasar ta hanyar mayar da jagorancin masarautar ga tsatsonsa, Saudiyya ta dauki matakin mika kai ga bakar siyasar yahudawan sahayoniyya tare da fara yin amfani da malaman fada domin fitar da fatawa da zata kare manufofin yahudawan, sakamakon haka Sheikh Ahmad bin Sa'id Al-Qarni ya fara bude fage a matsayin zakarar gwajin dafi, kuma matukar babu wata kwakkwarar maida martani daga al'ummar musulmin duniya musamman al'ummar Palasdinu, to babu shakka wannan mummunar dabi'ar makirci zata ci gaba da wanzuwa a tsakanin malaman fada da wata rana zata kai ga haramta duk wata gwagwarmayar Palasdinawa musamman kokarin 'yantar da kasarsu daga mamayar yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni