Majalisar Kwararru: Ranar Zabe Al'ummar Iran Za Su Sake Tabbatar Da Rikonsu Ga Tsarin Musulunci

Majalisar Kwararru: Ranar Zabe Al'ummar Iran Za Su Sake Tabbatar Da Rikonsu Ga Tsarin Musulunci

Shugaban majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar Iran Ayatullah Ahmad Jannati ya bayyana cewar ranar zabe mai zuwa al'ummar kasar Iran za su sake tabbatar wa da duniya ci gaba da rikon da suke yi wa tsarin Musulunci da ke iko a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya bayyana cewar Ayatullah Jannati ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda yace: A lokuta da dama al'ummar Iran sun tabbatar wa da duniya sanin ya kamatansu ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatarsu yayin gudanar da zabe, don haka a wannan Juma'ar ma za su sake fitowa don sauke wannan nauyi da ke wuyansu.

A bangare guda kuma shugaban majalisar kwararrun ya kirayi 'yan takaran zaben shugaban kasar da su ba da himma wajen magance matsalolin da al'umma suke fuskanta da kuma gudanar da tsarin tattalin arzikin dogaro da kai da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar.

A ranar Juma'ar nan mai zuwa, 19 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaben shugaban kasar na Iran karo na 12 tsakanin 'yan takara guda hudu, bayan da biyu daga cikin shida na farkon, wato magajin garin Tehran Muhammad Baqir Qalibaf da kuma mataimakin shugaban kasa Ishaq Jehangiri sun janye takarar na su da goya wa biyu daga cikin 'yan takaran wato Sayyid Ibrahim Ra'isi da kuma shugaba mai ci Hasan Ruhani baya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni