Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ta Fara Daukar Matakan Kuntatawa Kungiyar Hizbullah Na Kasar Lebanon

Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ta Fara Daukar Matakan Kuntatawa Kungiyar Hizbullah Na Kasar Lebanon

Majalisar dokokin Amurka "Congress" ta fara daukar matakan kuntatarwa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kuma kasashen da suke yakar yan ta'adda a yammacin Asia, ta hanyar samar da kudurori ko dokoki ukku.

Da farko dai, akwai gyaran fuskan da majalisar ta yiwa dokar hana kungiyar hizbullah samun kudade ta shekara ta 2017, da kuma abinda majalisar ta kira dokar hana kungiyar hizbullah amfani da fararen hula a matsayin garkuwa a yaki, sai kuma doka ta ukku, ta gabatar da bukata ga kasashen Turai na su sanya kungiyar Hizbullah cikin jerin kungiyoyin yan ta'adda a duniya.

Nasarorin a yaki da kuma ta siyasa wadanda kasashen da suke yakar kungiyar  Daesh da kawayenta a kasashen Lebanon, Syria da kuma Iraqi suka samu na daga cikin abubuwan da suka sanya gwamnatin kasar Amurka takurawa kasashen Iran, Syria da kuma kungiyar Hizbullah.

Amurka da kawayenta na kasashen Larabawa da kuma yankin, wadanda suka hada da Saudia da kuma HKI, sun damu kwarai da irin tasirin da kasar Iran da kuma kungiyar Hizbullah zake yi a fagen siyasa da kuma tsaro a yankin, musamman bayan nasarorin da suka samu kan kungiyar Daesh da kawayenta wadanda kasashen yamma da kawayensu a yankin suka samar don cimma mummunar manufofinsu a yankin.

Daga cikin matakan da Amurka ta dauka a wannan fagen dai, sun hada da raya ranar zagayoyowar kissan sojojin Amurkawa da aka yi a shekara ta 1983 a birnin Beyrout na kasar Lebanon a karon farko, inda a jawabin da ya gabatar a taron tunawa da wannan ranar, Mike Pence matainamkin shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa, shirin yaki da ta'adda na kasar Amurka a duniya ya tashi daga ranar 11 ga watan Satumban Shekara ta 2001 ya koma daga ranar 23 ga watan Octoban shekara ta 1983. Wannan matakin dai ya nuna cewa kungiyar al-qaeda, ba kuma barazana ce ga kasar Amurka ba, don haka a halin yanzu kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ce abar tuhuma.  

Sai dai kamar yadda kowa ya sani, kungiyar Hizbullah bangare ne karfi a gwamnatin kasar Lebanon, sannan tana da karbuwa a cikin mutanen kasar Musulmansu da sauran addinai, ba don kome bai sai don gwagwarmayan da take yi na kare kasar daga mamayar HKI da kuma khidimomin da take gabatarwa ga mutanen kasar wadanda suka hada da tallafawa marasa galihu na kasar.

Wadannan dokokin Congres ta samar dai suna nufin tuhumar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kisan fararen hula a kasar Syria don yakar yan ta'adda ta Daesh da take yi tare da sojojin kasar ta Syria.

Don haka wannan shi ne mataki na farko wanda  gwamnatin kasar Amurka da kawayenta na kasashen Larabawa da HKI zasu fara dauka don tabbatar da irin tsarin da suke bukata a kasashen  yammacin Asia. Amma sun tabbatar da cewa matukar kungiyar Hizbullah, da gwamnatocin kasashen Iran, Syria da Iraqi suna nan kamar yadda suke a halin yanzu, to kuwa  da wuya su cimma wadan nan mummunan manufofinta a yankin. Don wadan nan kasashene suka wargaza shirye-shiryen su na baya don cimma wannann gurin.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky