Mahajjatan Hajjin Bana A Nan JMI Zasu Fara Tafiya Kasa Mai Tsarki Daga Gobe Laraba

Mahajjatan Hajjin Bana A Nan JMI Zasu Fara Tafiya Kasa Mai Tsarki Daga Gobe Laraba

Shugaban hukumar hajji da ziyara a nan Iran ya bada sanarwan cewa a gobe Larabe ne tawaga ta farko na mahajjata daga kasar Iran zasu isa birnin Madina don fara ayyukan ibada na hajji da umra da kuma ziyara.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran Mohammad Muhammadi shugaban hukumar hajji da ziyara a nan kasar Iran ya bayyana cewa ya zuwa yanzu maniyyata dubu 25 suka sami visar aikin hajji da umra kuma sauran da yardar Allah zasu sami visarsu a cikin yan kwanaki masu zuwa. 

Labarin ya kara da cewa a hajjin bana dai maniyyata Iraniyawa dubu 85 da 200 zasu ya aikin hajji da umra. A ganawarsa da tawagar jami'ai masu kula da mahajjata a gidansa Jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa aikin hajji yana da muhimmanci, musamma a irin halin da musulmi suke ciki a duniya, don nan ne mahadar al-ummar musulmi na duniya gaba daya. Inda suke samun kusanci da juna da kuma tattauna matsalolinsu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky