Macron Zai Ziyarci Najeriya

Macron Zai Ziyarci Najeriya

A wani lokaci da yammacin yau Talata ne, ake sa ran shugaban kasar Faransa, Emanuel Macron, zai kai wata ziyarar aiki a Najeriya, wacce ita ce irinta ta farko wa wannan kasa renon ingila, tun bayan hawansa kan karagar mulki

An tsara Mista Macron, wanda zai barin birnin Nouakcott na kasar Mauritania, zai gana da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari, inda zasu tattauna kan batutuwa da dama ciki har da na tsaro.

Baya ga hakan kuma, Mista Macron zai  wuce zuwa birnin Legas, inda zai halarci dandalin Shrime na yaran Fela Kuti.

Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban kasar yamma dake kan mulki, zai sanya kafa a irin wannan waje na kide-kide da wake wake dake zaman cibiyar salon waka na ''afro-beat''.

Hukumomin Najeriya dana addinai a kasar, basa kallon wajen da daraja, kasancewar wuri ne na shaye-shayen muggan kwayoyi da kuma raye raye dake nuna tsaraici.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky