Macron Ya Tattauna Da Sarkin Saudiya Kan Kisan Khashoggi.

Macron Ya Tattauna Da Sarkin Saudiya Kan Kisan Khashoggi.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasar Faransa ta ce a daren jiya Laraba, shugaban kasar Emanuel Macron ya tattauna da sarkin Saudiya ta wayar talho kan kisan da aka yi wa Jamal Khashoggi dan jaridar nan da ya yi kaurin suna wajen sukan manufofin masarautar Saudiya

Sanarwar ta ce a yayin tattaunawar, Shugaban Macron ya tabbatar da cewa zai hada kai da abokin huldar kasar na ganin an kakaba takunkumi kan wadanda suka aikawa da wannan kisa.

Har ila yau Shugaban na Faransa ya bukaci karin haske daga kasar ta Saudiya kan yadda aka kashe Jamal Khashoggi.

A ranar talata 2 ga watan Oktoban da muke ciki ne, jamal Kashoggi ya je karamin ofishin jakadancin kasarsa ta haifuwa wato Saudiya domin karbar takardar saki na tsohuwar matarsa, domin yin wani auren a kasar Turkiya, daga wancan lokaci ba a kara jin labarinsa ba, inda aka zargi mahukuntan na saudiya da kashe shi.

Bayan matsin lamba da kasar Saudiyar ta fuskanta, a daren juma'ar da ya gabata, mahukuntan kasar ta Saudiya sun amsa laifinsu na kashe Jamal Khashoggi a karamin Ofishin jakadancin saudiya na birnin Istambul dake kasar Turkiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky