Limamin Tehran:Dogaro Da Nasihohin Imam Khumain Ne Ke Kare Juyin Musulunci

Limamin Tehran:Dogaro Da Nasihohin Imam Khumain Ne Ke Kare Juyin Musulunci

Ayatullah Sayyid Ali Khatami ya yi ishara da jagorancin da Imam Khomain y ayi wa juyin musulunci na Iran sannan ya ce babu yadda za a iya raba su

Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; A kodaushe al'ummar Iran suna cin arzikin sadaukar da kan Imam Khumain da jagorancinsa ne,kuma bisa dogaro da nasihohinsa ne juyin yake ci gaba.

Ayautullah Khamati ya kuma ce; A daidai wannan lokacin da ake bikin cika shekaru 39 da cin nasarar juyin musulunci, wajibi ne mu bayyana cewa; juyin wata ni'ima ce mai girma daga Allah ga duniyar musulunci musamman ga al'ummar Iran.

Limamin na Tehran ya bayyana Ayatullah Sayyid Ali Khamei a matsayin wanda yake ci gaba da jan ragamar juyi akan tafarkin da Imam Khumain ya shata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky