Limamin Tehran: Yin Gwagwarmaya Da Azzalumai Koyarwa Ce Ta Addini.

Limamin Tehran: Yin Gwagwarmaya Da Azzalumai Koyarwa Ce Ta Addini.

Ayatullah Muwahhidi Karmani da yake hubudar sallar juma'a ya ci gaba da cewa; Kalubalantar Dagutu makiya da Amurka ba batu ne na siyasa ba kadai, tunshesa addini ne.

Limamin na Tehran yana yin huduba ne akan zagayowar ranar 13 ga watan 8 na hijirar Shamshiyya wacce take a matsayin ranar fada da masu girman kai na duniya inda ya kara da cewa: A wannan lokacin na zagayowar ranar 13 ga watan Aban, wacce ita ce ta fada da masu girman kai da kuma kwace cibiyar leken asirin Amurka a Iran, wajibi in bayyana cewa; Rashin mika kai ga dagutu tushensa tauhidi ne.

Har ila yau limamin na Tehran ya yi nuni da ayar kur'ani da  Allah ya kasa mutane gida biyu, tsakanin masu bautar Allah da kuma masu bautar Dagutu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky