Larijani: Iran Za Ta Ci Gaba Da Tsayin Daka Wajen Tinkarar Kiyayyar Da Amurka Take Nuna Mata

Larijani: Iran Za Ta Ci Gaba Da Tsayin Daka Wajen Tinkarar Kiyayyar Da Amurka Take Nuna Mata

Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran, Dakta Ali Larijani, ya bayyana cewar Amurka ta kwana da sanin cewa al'ummar Iran za su ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar kiyayya da makirce-makirce da ita da haramtacciyar kasar Isra'ila suke kulla musu.

Dakta Larijani ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabin bude zaman majalisar a safiyar yau Lahadi, inda yayin da yake mayar da martani ga kalaman baya-bayan nan na shugaban Amurka ya bayyana cewar: A daidai lokacin da Donald Trump yake magana kan kakabawa Iran mafi tsananin takunkumi a daidai lokacin kuma yana magana kan yiyuwar tattaunawa da Iran don magance matsaloli.

Shugaban Majalisar shawarar Musuluncin ta Iran yayi watsi da wannan magana na tattaunawar yana mai cewa al'ummar Iran za su ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar wannan kiyayya da makircin da Amurkan ta ke kulla musu, kamar yadda kuma yayi watsi da kokarin da firayi ministan HKI Benjamin Netanyahu yake yi na neman daukin kasashen Turai wajen fada da Iran inda ya ce a wannan karon ma sahyoniyawan za su sha kashi a wannan makircin da suke kulla wa Iran.

A shekaran jiya ne shugaban Amurkan ya sake yin barazanar kakabawa Iran takunkumi mafi tsananin duk kuwa da ikirarin da yayi na cewa akwai yiyuwar Amurkan ta sake tattaunawa da Iran don cimma wata sabuwar yarjejeniyar nukiliya lamarin da kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran yayi watsi da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky