Kwamnatin jahar kaduna ta tuhumi Sheikh El-Zakzaky da laifin kisan kai

Kwamnatin jahar kaduna ta tuhumi Sheikh El-Zakzaky da laifin kisan kai

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a gaban kotu inda ta ke tuhumar jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'Yan Shi'a Sheik Ibrahim El-Zakzaky da kisan wani soji.

Kisan sojan na cikin tuhumce-tuhumce takwas da gwamnatin ta shigar a gaban kotun a kan malamin da wasu karin mutum uku.

Sauran mutanen biyu da ake zarginsu tare sun hada da Yakub Katsina da Sanusi Koki - shugabannin kungiyar a jihohin Katsina da Kano.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi arrangama da 'yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan Shi'a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan an yi awangaba da wasu da dama.

Tun daga lokacin ne hukumomi ke tsare da Sheikh Zakzaky da matarsa Zinatu a wani wuri da ba a bayyana ba, duk da cewa kotu ta bayar da izinin a sake su a lokuta daban daban.

  
Gwamnati jihar Kaduna ta kuma bayyana kungiyar a matsayin haramtaciyya kuma ta hanata yin taro a cikin jihar.

A farkon watan da mu ke ciki magoya bayan Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin lumana a kowace rana inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

Ibrahim El-zakzaky ya yi shekara biyu yana tsare ba tare an gurfanar da shi a gaban kotu ba, in ban da yanzu da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a gaban kotu.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tsare da jagoran 'yan na Shi'a da kuma matarsa soboda tsaron lafiyarsu.

A baya ta gabatar da su a gaban 'yan jarida inda malamin ya ce yana cikin koshin lafiya.

Ko da yake daga bisani lauyansa Femi Falana ya ce an shirya taron manema labaran ne ba tare da sanin jagoran 'yan Shi'ar ba.

Rahotanni sun ce idan aka samesu da laifi za a iya yanke mu su hukuncin kisa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky