Kungiyar Ansarullah Ta Mayar Da Martani Kan Shahadar Saleh Samad.

Kungiyar Ansarullah Ta Mayar Da Martani Kan Shahadar Saleh Samad.

Shugaban Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdul-malik Badaruddin Alhutsi ya sanar a jiya Litinin cewa za su bawa Ali sa'oud amsar da ta dace a game da kisan killar da su ka yi wa Saleh Samad shugaban majalisar kolin siyasar kasar.

Kafar watsa labaran Almasira ta kasar yemen ta nakalto Abdul-malik Badaruddin Alhutsi a jiya litinin ya ce Dakarun kawancen saudiya  da Amurka ne ke da alhakin shahadar Shugaban majalisar kolin siyasar kasar Saleh Samad, kuma wannan shahada ta shi za ta karawa Al'ummar kasar yemen juriya da karfin gwiwa na tunkarar kawancen saudiya dake kai hare-haren wuce gona da iri a kasar.

Shugaban Kungiyar Ansarullah ya tabbatar da cewa babu wani sakamako da masu wuce gona da irin za su cimma a game da shahadar Saleh Samad, sannan ya bukaci Al'umma da su fito dafifi domin halartar jana'izar ta shi.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce shugaban Majalisar koli ta siyasar kasar Yemen saleh samad ya yi shahada sanadiyar wani mumunan hari da jiragen yakin kawancen saudiya suka kai a jihar Hudaida.

Gwamnatin kasar ta Yemen ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar baki daya.

A ranar 6 ga watan Augustan 2016 aka zabi Saleh Samad, shugaban majalisar kolin siyasar kasar yemen, sannan a ranar 14 ga watan Augustan wannan shekara ya yi rantsuwar kama aiki a gaban 'yan majalisun kasar, inda nan take ya kama aikinsa


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky