Kotun Tarayya ta ba da umarnin 'a tsige Buhari'

Kotun Tarayya ta ba da umarnin 'a tsige Buhari'

Wata babbar kotu a Najeriya ta umarci majalisar dokokin kasar ta gaggauta fara aiwatar da bin matakan tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Alkalin babbar kotun da ke garin Osogbo jihar Osun ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba bisa karar da wasu 'yan Najeriya biyu suka shigar a gaban kotun.

Wani lauya Kanmi Ajibola da Sulaiman Adiniyi wani dan rajin kare hakkin dan Adam ne suka bukaci kotun ta ba majalisa umarnin gaggauta tsige Shugaba Buhari.

Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na Buhari na daga cikin bukatu hudu da mutanen biyu suka gabatar a gaban kotun, inda suke zargin shugaban da saba wa kundin tsarin mulkin kasar bayan rantsar da shi da takardun da suka kira na bogi.

Sai dai tun lokacin yakin zabensa ne kwalejin gwamnati a Katsina, inda Buhari ya kammala sakandare ta fitar da takardar shaidar kammala karatun a shekarar 1961.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky