Kioumars Heidari: Iran Tana Cikin Shirin Kare Kanta Daga Harin Wuce Gona Da Iri

Kioumars Heidari: Iran Tana Cikin Shirin Kare Kanta Daga Harin Wuce Gona Da Iri

Kwamandan rundunar sojin kasa ta kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin shirin ko-ta kwana domin maida martani kan duk wani harin wuce gona da iri da zata iya fuskanta daga makiya.

A zantawarsa da manema labarai a jiya Laraba: Kwamandan rundunar sojin kasa ta kasar Iran Brigadier Janar Kioumars Heidari ya jaddada cewa: Matakan da jami'an gwamnatin Amurka suke dauka na yada maganganu marassa tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zasu taba yin wani tasiri ba, amma duk da haka Iran tana cikin shirin kalubalantar duk wani harin wuce gona da iri da zata fuskanta daga makiyanta.

Heidari ya kara da cewa: Tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, Amurkawa suke kulla makirce-makirce kan kasar ta Iran, amma ci gaba da samun hadin kai a tsakanin al'ummar Iran da tsayin dakarsu kan kare manufofinsu zasu samu nasarar rusa duk wani makircin da ake kitsawa kansu.    ko


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky