Khatami: Manufar Amurka Rusa Tsarin Musulinci Na Kasar Iran

Khatami: Manufar Amurka Rusa Tsarin Musulinci Na Kasar Iran

Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na nan birnin Tehran ya bayyana cewa manufar magabatan Amurka rusa tsarin jamhuriyar musulinci ta Iran da kuma tsarin Wilayatul Fakih.

A yayin hudubar sallar Juma'a, Limamin da ya jagoranci sallar jum'a a nan birnin Tehran Ayatollah Ahmad Khatami ya bayyana cewa Amurka na  bayan kokarin ganin an illata tsarin jagoranci shugabanin Addini da ake kira da wilayatul-fakih da hakan ya sanya ta shirya tayar da yamutsi a yanki, tare da aiko da 'yan ta'adda gami da samar da gabas ta tsakiya babba wacce za ta yiwa magabatan na Amurka biyayya, wannan shiri na Amurka ba zai samu nasara har abada ba.

A yayin da yake magana kan dubarun Amurka a game da kasar Iran , Ayatollah Ahmad Khatami ya ce dubarun sun hada da dakatar da jamhoriyar musulinci ta Iran a game ci gaban da ta yi a bangaren shirin makaman nukiyarta na zaman lafiya, rage karfin tsaro da makamai masu lizzami, yanke alaka da kuma goyon bayan da kasar Iran take bawa kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon  da kungiyoyin gwagwarmaya na Palastinu, da kuma neman Iran ta amince da kafar yankin gabas ta tsakiya babba da ita Amurka take so, dukkanin wadannan dubaru ba su ci nasara ba.

Har ila yau, Ayatollahi Ahmad Khatami ya tabbatar da cewa dukkanin hukumomin kasar Iran sun hadu a kan cewa babu batun sake tattaunawa kan shirin nukiyar kasar na zaman lafiya, ko sake yi masa kwaskwarima, kuma ba za su amince da rage karfin tsaro na makamai masu lizzami da kasar ke kerawa ba, har ila yau ba za su taba barin wata kasa ta yi musu katsa landan a harkokin cikin gidan kasar ba.

Limamin da ya jagorancin sallar juma'a na nan birnin taheran ya ce jamhoriyar musulinci ta Iran tana aiki ne bisa tsarin musulinci da kuma dokokin kasar da suka bata damar taimakawa kungiyoyin gwagwarmayar Palastinu da Hizbullah ta kasar Kasar Lebanon.

Ayatollah Ahmad Khatami ya kara da cewa dubarun Amurka a yankin samar da rashin tsaro domin tabbatar da tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila, sannan ya ce a halin da ake cikin kasar Amurka na kai mayakan IS arewacin kasar Afghanistan domin tabbatar da manufofinta na tattalin arziki da siyasa.

A yayin da ya koma kan ta'addancin hukomomin Saudiya a kasar Yemen, da yanayin da kasar Bahrain ke ciki, Ayatollah Khatami ya ce yarima mai jiran gado na Saudiya ya mayar da kasar kamar wata jaha ta kasar Amurka, ita kuma gwamnatin kasar Bahrain ta mayar da kasar gidan yarin siyasa ta hanyar yanke hukunci kisa, daurin rai da rai da kuma kuma kwace takarun zama dan kasa ga manyan malamai na kasar mabiya mazhabar shi'a musaman ma babban malamin nan sheikh Isa Kasim


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky