Khan Ya Ayyana kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Pakistan

Khan Ya Ayyana kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Pakistan

Tsohon dan wasan kiriket Imran Khan ya yi ikirarin cewa ya lashe zaben kasar Pakistan a yayin da bangaren gwamnati suka zarginsa da tafka magudi a zaben.

Jam'iyyar da ke mulkin Pakistan ta ki amincewa da sakamakon farko na zaben da aka gudanar da ke nuna tsohon tauraron kwallon kiriket, Imran Khan ya kama hanyar zama sabon Firaministan kasar.

Shugaban Jam’iyyar Muslim League-Nawaz da ke mulkin Pakistan, Shahbaz Sharif ya yi watsi da sakamakon farko da aka fara bayyanawa a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’u.

Yayin ganawa da manema labarai a Lahore, Sharif ya ce, abin da suka gani na magudi ya mayar da Pakistan shekaru 30 baya, saboda haka ba za su amincewa da sakamakon zaben da aka bayyana ba.

Shi ma shugaban Jam’iyyar PPP, Bilawal Bhutto Zardari ya aike da sako ta Twitter da ke cewar 'yan takarar jam’iyyarsa na korafi kan cewa an kori wakilansu a tashoshin kidayar kuri’u, yayin da Jam’iyyar PML-N ta yi zargin cewa, jami’an tsaro sun karbe iko da tashoshin zaben.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky