Kashoggi : Trump Ya Nuna Gamsuwa Da Bayanin Saudiyya

Kashoggi : Trump Ya Nuna Gamsuwa Da Bayanin Saudiyya

Shugaba Donald Trump na Amurka ya nuna gamsuwarsa da bayannin da Saudiyya ta yi na cewa an kashe dan jaridan nan Jamel Kashoggi a cikin karamin ofishin jakadancinta na Santanbul.

Trump ya bayyana matakin Saudiyar a matsayin matakin farko mai kyau, kana ya nuna gamsuwarsa da bayananta inda ya ce akwai sahihanci a ciki.

Dama kafin hakan an sha yayata cewa Amurka na kokarin lullube batun don kare kawarta Saudiyya daga kisan na dan jaridan Khashoggi.

Wannan ne dai karon farko da masarautar Saudiyya ta amince da cewa Jamal Kashoggi ya mutu, sama da makwanni biyu bayan bacewar dan jaridan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky