Kashoggi : Ana Ci Gaba Da Matsin Lamba Wa Saudiyya

Kashoggi : Ana Ci Gaba Da Matsin Lamba Wa Saudiyya

Kasashen duniya na ci gaba da yin matsin lamba wa Saudiyya akan tayi bayyani kan bacewar dan jaridan nan Jamal Kashoggi wanda ake zargin an kashe shi a karamin ofishin jakadancinta na birnin Santambul a Turkiyya.

Matsin lambar dai ya fi fitowa ne daga kasashe aminnan Saudiyyar ciki harda Amurka da Faransa, duk da cewa kasashen sun ce wannan batun ba zai shafi hulda ko kwangilolin dake tsakaninsu da Saudiyyar ba.

A halin da ake ciki dai mahukuntan Saudiyya sun musunta zargin bada umurnin kashe dan jaridan, tare cewa a shirye suke su bada hadin kai a binciken da ake.

Tuni dai wasu manyan kamfanoni suka soke wasu kwagiloli da Saudiyyar, a yayin da kuma wasu manyan kafofin yada labarai suka sanar da janyewa daga halarta wani taron masu zuba jari da za a gudanar a wannan wata a birnin Riyadh na Saudiyar.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky