Kalaman Shugaba Buhari Kan Matasa Ya Janyo Ce-ce Ku-ce A Najeriya

Kalaman Shugaba Buhari Kan Matasa Ya Janyo Ce-ce Ku-ce A Najeriya

Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na cewa matasan kasar ba suyi karatu ba, kuma ba su da aikin yi, sannan suna jira gwamnati ta samar musu ababen more rayuwa da kudin mai ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin al'ummar kasar

A yayin jawabin da ya gabatar a taron kasashe renon Birtaniya da ke ci gaba da gudana a birnin London Muhammadu Buhari ya ce kimanin kaso 60 % na al’ummar kasar da galibinsu matasa ne, kashi 30 basu je makaranta ba, yayinda suke zaune kara zube bisa tunkahon kasarsu na da arzikin man fetur.

A cewar Muhammadu Buhari mafi yawa daga cikin matasan kasar, na jiran  gwamnati ne ta yi musu hidimar karatu, lafiya dama samar musu da muhalli kyauta ba tare da jibinsu ba.

Tuni dai kalaman na Muhammadu Buhari ya fuskanci mummunar suka  daga matasan wadanda suka ce shugaban bai musu adalci ba, ko da yake dai wasu na ganin akwai kanshin gaskiyar a batun na Muhammadu Buhari.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky