Juyayin Shahadar Imam Jafar Sadik (a.s)

Juyayin Shahadar Imam Jafar Sadik (a.s)

Musulman kasar Iran sun fara zaman makokin shahadar Imam Sadik (a) shugaban mazhabar shia Imamiya a daren yau a ko ina a duk fadin kasar.

A yau a Alhamis 25 ga watan shawwal ita ce ranara shahadar Imam Sadik (a) jikin manzon Allah (s) kuma limami na 6 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s).

Imam Jaafar bin Mohammad wanda ya fi shahara da Imam Sadiq (a) yana daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) wadanda suka sami damar yada addinin musulunci wanda kakakinsu ya zo da shi. Da shi da mahaifinsa Imam mohammad Al-baqir (a) sun bude jami'an mafi girma a madina a zamaninsu.

Malaman tarihi sun bayyana cewa Imam Sadik (a) yana da dalibai kimani 4000 wadanda suka dauki ilmi a wajensa, a fannonin ilmi da dama.

Muna mika ta'aziyyarmu ga dukkan musulmi musamman mabiya mazhabar Jaafariya dangane da wannan babban rashin da fatan Allah ya bamu cetonsu ranar da babu mai ceto sai da izinin Allah.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky