Jiragen yakin Saudiyya sun hallaka mutane sama da 7 a wani hari da suka kaiwa al'ummar Yamen

Jiragen yakin Saudiyya sun hallaka mutane sama da 7 a wani hari da suka kaiwa al'ummar Yamen

A ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin rundunar kawancen masarautar Saudiyya suke kai wa kan kasar Yamen a safiyar yau Litinin sun kashe mutane akalla bakwai.

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta kasar Yamen ta watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin rundunar kawancen masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan gidajen al'ummar yankin Hauran da ke lardin Al-Bayda na kasar Yamen a safiyar yau Litinin, inda suka kashe mutane akalla 7 tare da jikkata wasu 14 na daban.

Har ila yau jiragen saman yakin rundunar kawancen ta Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren ta'addanci kan yankunan lardin Sa'adah da ke shiyar arewa maso yammacin kasar ta Yamen, inda suka kashe tare da jikkata adadi mai yawa da ba a kai ga tantance su ba zuwa yanzu haka.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ce masarautar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen da nufin samun damar shimfida bakar siyasarta kan al'ummar kasar, inda ya zuwa yanzu ta kashe dubban mutane tare da tilastawa wasu miliyoyi yin gudun hijira.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky