Jiragen Yakin HKI Sun Yi Ruwan Boma Bomai Kan Yankin Gaza A Kasar Palasdinu Da Ta Mamaye

Jiragen Yakin HKI Sun Yi Ruwan Boma Bomai Kan Yankin Gaza A Kasar Palasdinu Da Ta Mamaye

Jaragen yakin HKI sun yi luguden wuta a kudancin yankin Gaza na kasar Palasdinu da ta mamaye a jiya da dare.

Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiya yahudawan tana cewa sojojin haramtacciyar kasar ta kai hare hare kan mayakan kungiyar Hamas a wurare daban daban a yankin ta kuma rusa wasu mashiga na karkashin kasa wadanda kungiyar ta tona.

Majiyar ta kara da cewa mayakan kungiyar Hamas sun maida martani da cilla rokoki kan yankunan yahudawan inda majiyar ta ce garkuwan makaman linzamin yahudan sun kakkabe biyar daga cikin rokokin sannan daya ya fadi a wani daji a kusa da matsugunan yahudawan.

Har ya zuwa yanzu dai babu bayanan irin asarori na rayuka da dukiyoyi da aka yi a hare haren jiragen yakin yahudawan a yankin na Gaza.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi na yahudawan suna tashi a lokacin kungiyar Hamas ta maida martani.

Tun ranar 30 ga watan Maris da ya gabata ne Palasdinawa suka fara tada bore a ko wace jumma'a don tabbatar da hakkin su na komawa gidajensu. Ya zuwa yanku dai Palasdinawa 140 suka yi shahada, daga cikinsu akwai yara ganana da dama.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky