Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Yi Luguden Wuta Kan Wata Cibiyar Lafiya A Yamen

Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Yi Luguden Wuta Kan Wata Cibiyar Lafiya A Yamen

Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan wata cibiyar lafiya a lardin Hajjah da ke yammacin kasar Yamen

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta kasar Yamen ta watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan wata cibiyar lafiya da take kauyen Mastaba da ke lardin Hajjah a shiyar arewacin kasar Yamen.

Har ila yau a daren jiya Litinin jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan wasu yankunan da suke lardin Hudaidah na kasar ta Yamen.

A gefe guda kuma sojojin Yamen da suke samun tallafin dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullahi ta kasar sun yi dauki ba dadi da sojojin hayar masarautar Saudiyya a garin Addarihami da ke kudancin lardin Hudaidah lamarin da ya janyo hasarar rayuka da jikkata a bangaren sojojin hayar na Saudiyya.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky