Jawabin Jagoran Juyin Islama A Birnin Mashhad

Jawabin Jagoran Juyin Islama A Birnin Mashhad

Jagoran juyin Islama na kasar Iran Ayatollah sayyid Ali Khameni ya gabatar da jawabia gaban dubban mutanen da suka taru a cikin hubbaren Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad, kamar yadda ya saba yi a farkon kowace shekara ta hijira shamsiyya.

Kamfanin dillancin labaran IRIB ya bayar da rahoton cewa, a yayin jawabin nasa, jagora ya jaddada muhimamncin mayar da hankali matukan batun bunkasa ayyukan kere-keren kamfanonin cikin gida, da kuma tabbatar da samar da guraben ayyuka ga matasa, domin bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar daga cikin gida.

Ya ce a kowane lokaci makiya suna amfani da makamin tattalin arziki ne da nufin raunana kasar Iran, duk kuwa da cewa bisa himmar masana da sauran ma'akata masu kwazo, da kuma taimakon Allah madaukkin sarki,a  cikin tsawon shekaru 37 na juyin Islama, makiya ba su iya cimma wannan buri nasu ba a kan jamhuriyar muslunci, a maimakon hakan a kullum tattalin arzikin kasar na ci gaba da bunkasa a matsayi na kasa da kasa.

Jagoran ya ci gaba da cewa a bangaren ayyukan tsaro hakika an samu gagarumin ci gaba, wanda da taimakon  Allah madaukakin sarki an cimma nasarori masu tarin yawa bangarori daban-daban na ayyukan tsaro.

Dangane batun zabuka kuwa, jagoran ya ce babban abin bukata shi ne al'umma su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar zabe, domin su zabi abin da su gamsu da shi, wanda shi ne hakikanin 'yanci da adalci wanda ke tsorata makiya dangane da damfaruwar al'umma da juyin Islama.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky