Janar Jafari ya Mayar Da Martani Kan Kokarin Amurka Na Bata Sunan Dakarun IRGC

Janar Jafari ya Mayar Da Martani Kan Kokarin Amurka Na Bata Sunan Dakarun IRGC

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluci na Iran (IRGC) Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana cewar bakin dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran da na Ma'aikatar harkokin wajen kasar sun zo daya a fagen kare manufofin juyin juya halin Musulunci yana mai kiran shugaban Amurka da ya fahimci hakan.

Janar Muhammad Ali Jafari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a bayan fagen taron hadin gwiwa na tsara yadda za a gudanar da bukukuwan shekaru 40 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar ta Iran inda yayin da yake magana kan barazanar shugaban Amurka Donald Trump yake ci gaba da yi a kan Iran da kuma dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar ya kamata Trump ya san cewa  wajen kare manufofin juyin juya hali kan bakin dakarun kare juyin da ma'aikatar harkokin waje da ma gwamnatin Iran duk daya ne.

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen na Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Iran za ta dau matakin mayar da martani kan wannan babban kuskure da shugaban Amurka Donald Trump zai yi na sanya dakarun kare juyin juya halin Musulunci cikin kungiyar 'yan ta'adda; yana mai cewa tuni ma dai an tsara matakan da za a dauka din wadanda za a aiwatar da su a lokacin da ya dace.

A ranar 15 ga watan nan na Oktoba ne ake sa ran shugaban Amurka zai sanar da matsayar gwamnatinsa kan yarjejeniyar nukiliya na Iran da kuma wasu batutuwa na daban da suka shafi Iran din ciki kuwa har da batun dakarun na IRGC da sanya su cikin kungiyar 'yan ta'adda lamarin da ya sanya babban kwamandan dakarun sanar da cewa matukar dai Amurka ta dau wannan matsayar to kuwa za su dauki dakarun Amurka da suke yankin nan tamkar 'yan kungiyar Daesh.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky