Janar Baqeri: An Hallaka Shugabannin 'Yan Daesh A Harin Da Dakarun Kare Juyi Suka Kai Abu Kamal

Janar Baqeri: An Hallaka Shugabannin 'Yan Daesh A Harin Da Dakarun Kare Juyi Suka Kai Abu Kamal

Babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana cewa harin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka kai sansanin 'yan ta'addan a Siriya wani mafari ne na daukar fansar jinin shahidan da 'yan ta'addan suka kashe a garin Ahwaz na Iran yana mai sanar da halakar wasu jagororin kungiyar Daesh a yayin harin.

Janar Muhammad Baqeri ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai inda yayin da yake karin haske dangane da harin da dakarun kare juyin suka kai ya bayyana cewar tun bayan harin ta'addancin da aka kai garin Ahwaz dakarun na Iran suka kaddamar da shirin daukar fansar jinin shahidan.

Har ila yau kuma yayin da yake sanar da halakar wasu jagororin kungiyar ta'addancin da ta shirya wannan harin, babban hafsan hafsoshin sojin na Iran ya kara da cewa harin mayar da martani da dakarun na IRGC suka kai, wani mataki ne na farko da za a ci gaba da yinsa har sai an dau fansar jinin shahidan a kan wadanda suka kai harin da kuma wadanda  suka shirya da kuma goyon bayansa yana mai bayyana cewar tsaron cikin Iran wani lamari ne da ba za a taba yin wasa da shi ba.

Kafin hakan ma dai babban kwamandan bangaren kare sararin samaniyya na Iran na dakarun kare juyin Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya ce dakarun Iran ba za su kasa a gwiwa ba wajen daukar duk wani matakin kare kasar daga duk wata barazana ta makiya.

A daren jiya Litinin ne dai dakarun kare juyin na Iran suka kai wa wani sansanin 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh da ke kasar Siriya hari da makamai masu linzami guda 6 da kuma wasu hare-hare da jirage marasa matuka inda suka hallaka da kuma raunana wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky