Jamus Na Duba Yiyuwar Bawa Iran Yuro Miliyon 300

Jamus Na Duba Yiyuwar Bawa Iran Yuro Miliyon 300

Jami'an gwamnatin kasar Jamus sun bayyana cewa gwamnatin kasar tana binciken yiyuwan mikawa kasar Iran kudadenta Yuru miliyon 300 don amfani da su a cikin gida

Jaridar Beelad na kasar Jamus ta bayyana a jiya litinin kan cewa ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Jamus da kuma na ma'ajiyar kudin kasar suna duba yiyuwan bawa Iran Yuru miliyon 300 daga cikin asusun ajiyarta a kasar don amfani da su a cikin gida. 

Jaridar ta kara da cewam sabanin ikrakin kasashen Amurka da kuma HKI na cewa Iran tana son amfani da kudadene wajen wasu ayyuka daban, jami'an gwamnatin Jamus suna ganin babu alamun hakan ko kuma wannan zargin. 

Kafin haka dai gwamnatin kasar Iran ta bukaci kasashen Turai musamman wadanda suka rattaba hannu da ita kan yerjejeniyar shirin nukliyar kasar, su nuna cewa da gaske suna son wanzuwar wannan yerjejeniyar a aikace bayan da gwamnatin Amurka ta yi watsi da ita a cikin watan mayun da ya gabata. Banda haka gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa kasashen turai da suka sanyawa yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran tare da ita rashan zasu bude wata hanyar kasuwanci da Iran ba tare da dalar Amurka ta shiga tsakanin ba, don kodaitar da Iran ci gaba da mutunta yerjejeniyar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky