Jami'an Tsaron Masar Sun Kashe 'Yan Kungiyar Hasm A Yankin Arewacin Alkahira Na Kasar

Jami'an Tsaron Masar Sun Kashe 'Yan Kungiyar Hasm A Yankin Arewacin Alkahira Na Kasar

Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Masar da 'yan kungiyar Hasm bangaren sojin kungiyar Ihawanul- Muslimin ta kasar ya lashe rayukan mutane biyar a lardin Qalyubia da ke arewacin birnin Alkahira na kasar.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar a cikin daren jiya Talata ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi dauki ba dadi da gungun 'yan kungiyar Hasm bangaren sojin kungiyar Ihwanul-Muslimin ta kasar a yankin Al-Ubur da ke lardin Qalyubia a arewacin birnin Alkahira, inda jami'an tsaron na Masar suka kashe 'yan kungiyar ta Hasm biyar.

Har ila yau sanarwar ta fayyace cewa: An kama 'yan kungiyar ta Hasm biyar a yankin El-Marg da ke gabashin birnin na Alkahira. Kamar yadda a farkon watan Yunin wannan shekara jami'an tsaron na Masar suka kashe 'yan kungiyar ta Hasm guda 10. Tuni dai gwamnatin Masar ta sanya sunan kungiyar Hasm cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.   


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky