?>

Jami’an tsaro sun tarwatsa masu taron tunawa da Shahidan Quds 2014

Jami’an tsaro sun tarwatsa masu taron tunawa da Shahidan Quds 2014

A yau ne da gamayyan jami’an tsaron da suka hada da Mopol da ‘yan sanda da sojoji suka zo farfajiyar filin Darur Rahma dake a kan hanyar zuwa Jos a lokacin da ake yin taro domin tunawa da ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da sojoji suka kashe a Muzaharan Quds ta 2014 suka umurci kowa da kowa da ya watse a ya bar wajen.
Jami’an tsaron da suka je Darur Rahma domin tarwatsa masu wannan taro sun kai kimanin mota 8 zuwa 10 dauke da muggan makamai suna umartan mahalarta taron da su bar wajen taron.
Ganin haka ya sanya jagororin taron suka yi addu’a suka ziyarci shahidan dake kwance a wajen,sannan suka fito daga wajen cikin natsuwa,su kuma jami’an tsaron gefe guda suna bin su a baya har suka fito bakin titi suka hau ababen hawansu suka tafi suka bar wajen.
A lokacin da majiyarmu ta tuntubi AC din Zariya,ACP Ibrahim akan ko me yasa jami’an tsaro suka je wajen wannan taro domin su hana shi?Sai yace : “akwai matsala ne a wajen shi yasa suka basu shawara su bar wajen.”
Shi kuma Sheikh Abdulhamid Bello,daya daga cikin jagororin wannan taro cewa yayi:
“Mun saba duk shekara muna shirya irin wannan taro domin tunawa da ‘yan uwanmu su 34,ciki har da ‘ya’yan jagoranmu guda uku da aka kashe a shekarar 2014.
“Mun fara taron da karfe 8:00 na safe,can wajen karfe 10:00 na safe sai ga jami’an tsaro sun zo sun same mu,da farko sun fara zagaye mu ne ba tare da sun ce komai ba,sai muka cigaba da taron mu.
“Zuwan ‘yan sanda karkashin jagorancin ACP ked a wahala,sai suka fara kawo mana cikas a taron,sun ta kokarin su sa mu harzuka amma ba suyi nasara ba.Sai suka zo suka cewa mai wa’azi ba damuwa,yi ka gama ka karkare ku tashi ku bar wajen.”
Sheikh Bello ya sheda ma majiyarmu cewa taron ya samu halartan almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwan kusa da nisa kuma anyi jawabai masu yawa kafin zuwan jami’an tsaro su kawo cikas

Zaria

Zaria

Zaria

Zaria

Zaria

Zaria


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*