Jagoran Juyin Musulunc Yace Iran Ta Tsaya Ken Gaban Makiyanta

Jagoran Juyin Musulunc Yace  Iran Ta Tsaya Ken Gaban Makiyanta

Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Ali khamna'i ya bayyana cewa Kasar Ta Iran Ta tsaya kyam a gaban kasashe masu girman kai na duniya kimanin shekaru 40

Tashar talabijon ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Jagoran ya fadi haka ne a yau Alhamis a lokacin da yake ganawa da mahaddatan Al-qur'ani mai girma wadanda suka halarci gasar karatun Al-qur'ani karu na 35 a nan Tehran.

Jagoran ya kara da cewa yakamata al-ummar musulmi su fahinci karatun an-qur'ani mai girma su kuma aiwatar da shi bayan haddarsa. Hanya daya tilo ta daukkakar musulmi a duniya ita ce aiwatar da shiriyar Allah da ke cikin al-qur'ani mai girma Inji jagoran.

Daga karshe jagoran ya bada misali da zancen shugaban kasar Amurka na baya bayan nan, kan cewa wasu kasashen gabas ta tsakiya ba za su wanzu na tsawon mako guda ba, in ba tare da taimakon Amurka ba, wannan na daga cikin illolin nisantar karantarwan Alqur'ani mai girma, wanda wasu kasashen musulmi suka yi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

asura-mystery-of-creation
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky