Jagora Ya Bukaci Ma'aikatar Shari'ar Iran Ta Bayyana Matsayinta Kan Harkokin Da Suke Gudana A Duniya

Jagora Ya Bukaci Ma'aikatar Shari'ar Iran Ta Bayyana Matsayinta Kan Harkokin Da Suke Gudana A Duniya

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya yi kira ga ma'aikatar shari'ar kasar da ta fito ta bayyana matsayinta kan harkokin da suke gudanar a duniya.

A ganawarsa da alkalin alkalan kasar Iran Ayatullahi Sadiq Amuli Larijani da manyan jami'an ma'aikatar shari'ar kasar a jiya Litinin: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya jaddada cewa: Dole ne a kan ma'aikatar shari'ar Iran shiga fagen harkokin da suke gudanar a duniya domin bayyana matsayinta a bisa mahangar doka misali bayyana matsayinta kan takunkumin zalunci da ake kakaba wa kasashe, tsare kudaden kasar Iran da Amurka ke yi, ayyukan ta'addanci da ke addabar duniya, goyon bayan al'ummun da ake zalunta kamar musulmin Mayanmar da na Kashmir da taimakawa mutanen da ake zalunta a duniya kamar Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaki.

Har ila yau Jagoran Juyin Juya Halin na Musulunci ya fayyace cewa: Daukan matakin doka domin bin kadin irin wadannan al'amura a matakin kasa da kasa yana da muhimmanci kwarai, kamar yadda bayyana matsayin ma'aikatar ta shari'a kan goyon bayan masu hakki da yin tofin Allah tsine kan azzalumai ke da gagarumin tasiri a fagen rayuwa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky