Jagora Ya Bukaci Gwamnatin Iran Da Ta Gaggauta Taimakon Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Ritsa Da Su

Jagora Ya Bukaci Gwamnatin Iran Da Ta Gaggauta Taimakon Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Ritsa Da Su

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci gwamnatin Iran da ta gaggauta taimakawa mutanen da ambaliyar ruwar da ta faru a lardunan Azarbaijan ta gabas da ta yamma ta kasar Iran don magance musu irin matsalolin da suke ciki.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne cikin wani sakon ta'aziyya da ya fitar biyo bayan faruwar ambaliyar ruwar, inda yayin da yake isar da sakon ta'aziyya da juyayinsa ga iyalai da 'yan'uwan wadanda ambaliyar ruwar ta ritsa da su inda ya ce nauyin da ke wuyan jami'an da abin ya shafa shi ne taimakon wadanda abin ya shafa cikin gaggawa don rage musu irin damuwa da matsalolin da suke ciki.

A wani bangare na sakon nasa, Ayatullah Khamenei yayi addu'ar neman rahama da gafarar Ubangiji ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka sami raunuka.

Ambaliyar ruwar dai ta faru ne sakamakon irin ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi a lardunan Azarbaijan ta Gabas da ta yamma lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 36 baya ga wadanda suka sami raunuka da kuma hasarar dukiya da aka yi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky