Jagora Ya Bada Umurnin Hanzarta Hukunta Masu Hannu A Barnata Dukiyar Kasar Iran

Jagora Ya Bada Umurnin Hanzarta Hukunta Masu Hannu A Barnata Dukiyar Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bada umurnin hanzarta daukan matakin hukunta mutanen da aka kama da hannu a barnata dukiyar kasa a Iran.

A amsarsa ga wasikar da alkalin alkalai na kasar Iran Ayatullahi Sadiq Amuli Larijani ya aike masa: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i a jiya Asabar ya bada umurnin hanzarta daukan matakin hukunta duk wadanda aka samu da hannu a barnata dukiyar kasa.

A sakon wasikar da ya aike ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran: Alkalin alkalan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatullahi Sadiq Amuli Larijani ya fayyace cewa: A daidai lokacin da makiya al'ummar Iran suka kunna wutan yakin tattalin arziki kan kasar Iran amma ana samun wasu mabarnata da bata gari suna zagon kasa ga harkar tattalin arzikin Iran tare da karfafa mummunar aniyar makiya, sakamakon haka ma'aikatar shari'a tana bukatar izini na musamman kan daukan kwararan matakai da zasu kawo karshen irin wannan barna a cikin kasa.

Har ila yau amsar da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya gabatar ya jaddada bukatar cewa: Kada ma'aikatar shari'a ta kuskura ta yi sassauci ko rangwame kan duk wanda aka samu da hannu a barnata dukiyar kasa ko zagon kasa ga harkar tattalin arzikin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky