Jagora: Tattaunawa Da Amurka Ba Ta Da Amfani

Jagora: Tattaunawa Da Amurka Ba Ta Da Amfani

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa tattaunawa da Amurka ba ta da wani amfani, amma ana iya ci gaba da tattaunawa da kasashen turai.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran ya na fadara haka ne a jiya Asabar a lokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar da kuma sauran jami'an diblomasiyyar kasar a gidansa.

Aya. Khaminae ya kara da cewa babu abinda Amurka take bukata in banda tumbuke JMI sannan Iran ta zama kamar yadda take da Amurka kafin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar. Ya ce a halin yanzu akwai wasu kasashen duniya a Asia da Afrika wadanda suke hulda da kasar Amurka amma kuma suke cikin mummunan hali, dangantakarsu da Amurka bata tsinana masu kome ba.

Daga karshe jagoran ya jaddada cewa tattaunawa da Amurka babban kuskure ne, don ita ba abar dogaro ne ba, bissa duk wani alkawarin da ta dauka.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky