Jagora: Taron Ranar 22 Ga Watan Bahman Na Bana Zai Fi Na Bara Yawan Jama'a.

Jagora: Taron Ranar 22 Ga Watan Bahman Na Bana Zai Fi Na Bara Yawan Jama'a.

Jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa ranaikun ubangiji da kuma tarurruka masu mahimanci na tunawa da juyin juya halin musulinci na kara karfafa tsarin musulinci sannan ya tabbatar da cewa da yardar Ubangiji, ranar tunawa da cin nasarar juyin juya halin musulinci na bana zai fi na ko wata shekara kuma zai zamanto abin sha'awa.

A yayin ganawarsa da manyan sojojin sama na kasar a daidai rana mai tarihi na meka wuya da sojojin saman kasar suka yi ga Imam Khomeini a ranar 19 ga watan Bahman na shekarar 1357 h, k, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa shekarar bana, al'ummar Iran za ta fito fiye da shekarun da suka gabata saboda irin kalaman da wasu hukuomin Amurka da wasu kasashe ke yi na raunana juyin juya halin musulinci, domin a wannan lokaci al'umma na jin irin tarkon da makiya ke yi na ci gaba da kuma kara nuna kiyayarsu a fili.

 Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya ce a yau al'ummar kasar Iran, sun fi wadanda wadanda suka gabata tsayin daka da basira  gami da hangen nesa wajen kare juyin musulinci, domin haka juyin juya halin musulinci a yau ya samu ci gaba da kamala.

Jagoran juyin juya halin musulunci ya kara da cewa juriya da kuma tsayin daka wajen kalubalantar zalinci da fasadi a duniya shi ne tushen siyasar masu riko da addini, a yau, wanda yafi kowa zalinci da  rashin tausayi a duniya, ita ce gwamnatin Amurka kai sun fi kungiyar ta'addancin nan ta ISIS rashin imani da kuma dabbanci.

A matsayin tuni, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa hukumomin Amurka sune suka samar da kungiyar ISIS kuma su suke basu kariya, makamai da kudade, sannan suna farfagandar cewa sune masu kare hakin bil-adama, da wadanda aka zalinta har ma da dabbobi, to kamata ya yi su ji kunya bayan da gaskiya ta bayyana.

Jagora ya bayyana shekaru 70 na goyon bayan zalincin da ake yiwa al'ummar Palastinu, da kuma goyon bayan kisan al'ummar yemen da zalintarsu a matsayin misali na zalincin Amurka, sannan ya kara da cewa a ko wata rana ta a.. ana yi ruwan bama-bamai a kan gidaje da al'ummar kasar yemen da jiragen yaki da makaman Amurka , amma duk da hakan hukumomin Amurka ba su taba nuna wata damuwa ba, amma kuma kunya ba su ji ba, suka nuna wasu birbidin karfe ba tare da wani dalili ba suka yi da'awar cewa wai makami mai linzamin kasar Iran ne ta baiwa mayakan Hutsi suka harba birnin Riyad na saudiya.

A yayin da yake ishara a game da misali na tsayin daka na jamhoriyar musulinci ta Iran wajen tunkarar zalinci a yankin, Ayatollahi sayyid Ali Khanenei ya ce a game da batun gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya, hukumomin Amurka sun yi iya nasu kokari wajen karya lagon gwagwarmaya, amma muka nuna juriya, muka kuma ce ba za mu taba basu damar hakan ba, kuma a yau Duniya ta tabbatar da cewa Amurka ta so, kuma ta kasa, mu kuma mun so, kuma mun aiwatar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky