Jagora: Shishigin Makiya A Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Tsanani

Jagora: Shishigin Makiya A Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Tsanani

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi makiya jamhuriyar muslunci da su yi hattara a kan duk wani gigin yin shishigi a kan Iran, domin kuwa hakan zai fuskanci martani mai tsanani.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar bikin yaye wasu jami'an tsaro, inda ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da gudanar da dukkanin ayyukanta a bangarorin kimiyya da fasaha da kuma tsaro, duk kuwa da matsin lambar da take fuskanta daga kasashe masu girman kai da kuma 'yan korensu.

Jagoran ya kara da cewa, babbar matsalar da kasashe masu girman suke da ita a kan Iran ita ce, Iran kasa mai cikakken 'yancin siyasa, wadda ba ta mika wuya ga bakaken manufofinsu, bugu da kari kuma bisa taimakon Allah ta samu dogaro da kanta maimakon dogara da su.

Dangane da batun zabe mai zuwa kuwa, jagoran ya kirayi dukkanin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu wajen kada kuri'unsu, tare da kiyaye dokoki da ka'idojin da aka saka, domin tabbatar da cewa komai ya gudana a cikin tsari.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky