Jagora: Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Duk Wani Karan Tsaye Ga Yarjejeniyar Nukiliya

Jagora: Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Duk Wani Karan Tsaye Ga Yarjejeniyar Nukiliya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunne da cewa Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya da ta cimma da kasashen kungiyar 5+1, to sai dai za ta mayar da martani ga duk wani karen tsaye ga yarjejeniyar.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi wajen bikin yaye daliban makarantar 'yan sanda ta Iran, inda yayin da yake magana kan yarjejeniyar nukiliyan ya ce al'ummar Iran suna nan tsaye kyam kan kafafunsu kan yarjejeniyar nukiliyan, to amma duk wani kokarin karya yarjejeniyar daga wajen ma'abota girman kan duniya zai fuskanci mayar da martanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan yayin da yake magana kan maganganun da matakan da gwamnatin Amurka take dauka dangane da yarjejeniyar nukiliyan, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Amurkawa suna nuna wannan mugunta da kiyayya ta bangarori daban-daban dangane da wannan batu na yarjejeniyar nukiliya, wanda hakan yana dada tabbatar da abin  da Imam Khumaini (r.a) ya fadi dangane da Amurkan ne na cewa ita Babbar Shaidaniya ce. 

Ayatullah Khamenei ya ce Iran ta fara shirin nukiliyanta na zaman lafiya ne bayan da masanan kasar suka ce tana bukatar alal akalla megawatt 20,000 na makamashin nukiliya din, to amma Amurka tana adawa da hakan saboda tsohuwar gabar da take da shi kan duk wani abin ci gaba na al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniya.

Yayin da ya koma kan batun matsalar tsaro da ake fuskantar a yankin nan kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya dora alhakin hakan kan Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila saboda bakar aniyar da suke da ita na mamaya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky