Jagora : Ian Da Rai Na Iran Ba Za Ta Taba Mika Wuya Ga Makiya Ba

Jagora : Ian Da Rai Na Iran Ba Za Ta Taba Mika  Wuya  Ga Makiya  Ba

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa, ba zai taba yarde wa mika Iran ba ga makiya.

Da yake bayyana hakan yau Alhamis a wani jawabinsa gaban dakarun sa kai na (Bassij), jagoran ya kara da cewa muddun ina raye kuma ina cikin koshin lafiya, da kuma taimakonku, ba zan taba yarde mika wannan kasa ba ga makiya ba. 

Wanann a cewar Jagoran tamakar cin amana ne ga al'ummar Jamhuriya musulinci ta Iran.

A daya bangaren kuma jagoran ya ce, da yardar Allah Iran zatayi nasara kan takunkuman Amurka, wanda kuma hakan zai nuna kasawar Amurka.

Kimanin dakarun sa kai 150,000 ne suka hadu a filin kwallo na Tehran, a yau, wanda kuma suke shirye domin shiga lungu da tsako na kasar domin taimakawa ayyukan tsaron al'umma da dukiyoyinsu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky