Jagora: Babu Tattaunawa Da Amurka A Lokacinda Take Takurawa Da Kuma Nuna Fin Karfi Ga Iran

Jagora: Babu Tattaunawa Da Amurka A Lokacinda Take Takurawa Da Kuma Nuna Fin Karfi Ga Iran

Jagoran juyin juya halin musulunci aya Sayyid Aliyul Khaminei ya bayyana cewa kasar Iran ba zata shiga tattaunawa da kasar Amurka a dai dai lokacinda ta dabaibaye kasar da takunkumai ko kuma take nuna fin karfi wa kasar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a yau litinin a lokacinda ya ke ganawa da wasu mutae da suka kai masa ziyara a gidansa. 

Aya. Khaminai ya kara da cewa tattaunawa da Amurka a halin yanzu ba mai yuwa ba ne, ba don kome ba don sanin halayyar gwamnatin Amurka na rashin cika alkawari da kuma sabawa duk yerjejeniyar da aka cimma da ita. Kekyawar misili shi ne yerjejeniyar shekara ta 2015 wacce gwamnatin Amurka mai ci ta fice daga yerjejeniyar sannan ta bukaci a sake tattaunawa. 

Dangane da matsalolin tattalin arzikin da kasar Iran ta fada cikin a cikin yan watannin da suka gabata kuma, jagoran ya bayyana cewa matsaloli ne na cikin gida, matsaloli wadanda suka hada da rashin kula da harkokin tattalin arzikin kasar kamar yadda ya dace daga bangaren jami'an gwamnati da kuma wadanda suke zagon kasa wa tattalin arzikin kasar daga cikin gida. Daga karshe jagoran ya bukaci a gaggauta hukunta wadanda aka kama da hannun a cikin gurgurta tattalin arzikin kasar.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky