Jagora: Amurka Ta Shigo Da Daesh A Cikin Afganistan Ne Don Halastawa Kanta Ci Gaba Da Kansacewa A Yankin

Jagora: Amurka Ta Shigo Da Daesh A Cikin Afganistan Ne Don Halastawa Kanta Ci Gaba Da Kansacewa A Yankin

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, bayan ya isar da ta'aziyyarsa ga mutanen kasar Afghanistan kan hare-haren ta'addancin da ya lashe rayukan mutane da dama a cikin kwanakin nan, ya ce Amurka ce take karfafa yan Taliban a kasar.

Majiyar muryar Jamhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a safiyar yau Talata, ya kuma kara da cewa tun lokacin da aka sami nasarar korar  kungiyar yan ta'adda ta Daesh daga kasashen Iraqi da Syria Amurka ta fara daukar su daga gabas ta tsakiya zuwa kudancin Asia, don halasta samuwarta a yankin.

Jagoran ya kara da cewa gwanatin kasar Amurka ta mamaye kasar Afghanistan tun shekara ta 2001, wato shekaru 17 da suka gabata, da sunan yaki da kungiyar Al-qaeda, amma tun lokaci mutanen kasar ba su sake samun zaman lafiya ba. 

Dubban mutanen Afghanistan ne suka rasa rayukansu a cikin yan watannin da suka gabata sanadiyyar hare-haren kungiyar Daesh da kuma Taliban, wadanda dukkaninsu Amurka ce ta samar da su.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky