Iran:Hasan Rauhani Ya Saba layar Kama Aiki A Zango Na Biyu Na Shugabancin Kasar Iran

Iran:Hasan Rauhani Ya Saba layar Kama Aiki A Zango Na Biyu Na Shugabancin Kasar Iran

Dr.Hassan Rauhani wanda shi ne shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na 7 ya rantse akan zai kare musulunci da tsarin jamhuriyar musulunci da tsarin mulkin kasa

Bikin rantsar da shugaban kasar an yi shi ne a cikin ginin Majalisar shawarar musulunci a gaban babban alkalin alkalai Ayatullah Sadik Amuli Larijani, da kuma 'yan majalisar shawarar musulunci da mambobin majalisar kare tsarin mulki, da bakin da su ka zo daga kasashen waje.

Rauhani ya rantse da cewa; zai kare mazhabar kasa, da tsarin jamhuriyar musulunci da tsarin mulkin kasa, kuma zai yi aiki da dukkanin ikon da ya ke da shi wajen sauke nauyin da ya ke wuyansa da yi wa mutane hidima da daukaka matsayin kasa. Haka nan watsa addini da kyawawan halaye da goyon bayan gaskiya da kuma kare 'yancin da mutuminci mutane da hakkokinsu kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanada.

Da akwai baki daga cikin gida da kuma waje fiye da tawaga 100 da su ka halarci bikin rantsar da shugaban na Jamhuriyar musulunci ta Iran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky