Iran: Za A Fara Neman Ganin Jaririn Wata Ramadan Da Yammacin Yau Juma'a

Iran: Za A Fara Neman Ganin Jaririn Wata Ramadan Da Yammacin Yau Juma'a

Shugaban cibiyar neman jaririn watan a gundumar Yazd ya sanar da tura kungiyoyin kwararru hudu zuwa sassan daban-daban na gundumar domin ganin jaririn watan.

Shugaban cibiyar neman jaririn watan a gundumar Yazd ya sanar da tura kungiyoyin kwararru hudu zuwa sassan daban-daban na gundumar domin ganin jaririn watan.

A yau juma'a ne Hujjatul-Islam Ali Ridha Sharifi ya fadawa kamfanin dillancin labarun Irna cewa; A cikin wadannan gungu-gungu na mutane,da akwai kwararru 20 da su ka hada masana ilimin falaki.

Mutanen za su zauna a kauyukan Ardkan, Mubid, da kuma wani sashe na kauyen Taft domin sa ido akan fitowar jaririn watan gabanin faduwar ranar yau juma'a.

Sharifi ya ci gaba da cewa; Saboda ba abu ne mai yiyuwa  ba a iya ganin jaririn watan kai tsaye da idanu a gundumar ta Yazd, kungiyoyin za su yi amfani da na'urorin zamani na hangen nesa.

Kungiyoyin da su ke aiki a gundumar ta Yazd, suna a karkashin  cibiyar ganin watan azumi ne ta kasa.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky