Iran: Tsoma Bakin Kasar Amurka A Harkokin Cikin Gidan Afganistan Yana Kara Rusa Kasar

Iran: Tsoma Bakin Kasar Amurka A Harkokin Cikin Gidan Afganistan Yana Kara Rusa Kasar

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da kungiyar ta'addanci ta Taliban ta kaddamar kan sojojin gwamnatin Afganistan a ranar Juma'ar da ta gabata.

A bayanin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahrom Qasimi ya fitar a jiya Asabar yana dauke da tsananin bakin ciki da nuna alhini kan kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi wa sojojin gwamnatin Afganistan kimanin 150 a kusa da Mazari -Sharif da ke lardin Balkh; Yana mai jaddada cewar dole ne kasar Amurka ta kawo karshen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar ta Afganistan.

Bahrom Qasimi ya jaddada cewa: Hanyar kawo karshen matsalolin tashe-tashen hankula a Afganistan ita ce; janyewar sojojin mamaya daga cikin kasar domin bai wa gwamnatin Afganistan damar warware duk wata takaddamar siyasa tsakanin kungiyoyin kasar ta hanyar tattaunawa da zata kai ga kafa gwamnatin hadin kan kasa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Taliban na mutane goma suka farma Masallacin Juma'ar rundunar sojin Afganistan da ke kusa da Mazare-Sharif a lardin Balkh, inda biyu daga cikinsu suka tarwatsa kansu a tsakanin sojojin da suka zo sallar Juma'a sannan sauran takwas suka dauki matakin bude wuta kan mai uwa da wabi kan jama'a lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwan mutane kimanin 150 tare da jikkatan wasu fiye da 80 na daban. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky