Iran Tace A Shirye Take Ta Hada Hannu Da Saudiyya Wajen Karfafa Gabas Ta Tsakiya

Iran Tace A Shirye Take Ta Hada Hannu Da Saudiyya Wajen Karfafa Gabas Ta Tsakiya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana aniyarta na hada hannu da kasar Saudiyya wajen karfafa yankin Gabas ta tsakiya da kuma kawo karshen irin wulakancin da Amurka take yi wa kasashen yankin.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ne ya bayyana hakan a wani sako da ya rubuta a shafinta na Twitter inda ya ce: Shugaba Trump ya sha wulakanta Saudiyyawa yana cewa ba za su iya ci gaba da wanzuwa ba sama da sati biyu ba tare da taimakon Amurka ba.

Dakta Zarif ya ci gaba da cewa: Hakan shi ne sakamakon mika kula da tsaron kasa ga 'yan kasashen waje. Don haka muna sake mika hannuwanmu ga makwabtanmu cewa: Ku zo mu karfafa yankin nan da kanmu, sannan mu kawo karshen irin wannan wulakanci na ma'abota girman kai.

A kwanakin baya ne dai shugaba Amurka, Donald Trump a yayin yakin neman zabe ya ce ya shaida wa sarkin Saudiyya, Sarki Salman cewa idan ba don taimakon Amurka ba zai ci gaba da wanzuwa na sama da makonni biyu ba, don haka wajibi ne ya biya Amurka kudin da take kashewa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky