Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kan Masallacin Juma'a A Kasar Afganistan

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kan Masallacin Juma'a A Kasar Afganistan

Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai wani Masallacin Juma'a a lardin Paktia na kasar Afganistan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi ya mika sakon ta'aziyya da alhinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga gwamnatin Afganistan da al'ummar kasar musamman iyalan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin ta'addancin da aka kai cikin Masallacin Juma'a na mabiya mazhabar shi'a a garin Gardez da ke lardin Paktia na kasar Afganistan a jiya Juma'a.

Qasimi ya kara da cewa: Mummunar manufar masu dauke da akidar kafirta musulmi ita ce; kokarin ganin sun raba kan al'ummar musulmi tare da cusa dabi'ar tsoro da firgita a cikin zukatan al'ummar kasar, amma matukar gwamnatin Afganistan da al'ummar kasar suka fadaka tare da aiki tare, to babu makawa zasu rusa duk wani makirci da ake kitsawa kan kasarsu.

A jiya Juma'a ce wasu gungun 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirta musulmi suka kai harin wuce gona da iri kan Masallacin Juma'a na Imamuz- Zaman Al-Mahdi {a.s} na mabiya mazhabar shi'a da ke garin Gardez a lardin Paktia na kasar Afganistan, inda suka bude wutan bindiga kan masallata sannan suka tarwatsa kansu da bama-bamai da suka yi jigida da su lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 31 tare da jikkatan wasu fiye da 80 na daban.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky