Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai Birnin Kabul Na Kasar Afganistan

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai Birnin Kabul Na Kasar Afganistan

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wata makaranta a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Bahroum Qasimi ya yi tofin Allah tsine kan harin kunan bakin waken da aka kai wata makaranta da ke yammacin birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan a jiya Laraba tare da mika ta'aziyya da alhinin kasar Iran ga gwamnatin Afganistan da al'ummar kasar musamman iyalan mutanen da harin ya ritsa da su.

A jiya Laraba ce wani dan kunan bakin wake da ya yi jigida da bama-bamai ya tarwatsa kansa a wata cibiyar ilimi a yankin Dashte Barchi da ke shiyar yammacin birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 48 tare da jikkata wasu fiye da 67 na daban.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky